RANA MAFI KUNCI A RAYUWATA.
Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga mahaliccin duniyoyi wanda ya aiko manzonsa muhammad S.A.W zuwa doniya bakidaya. tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabi muhammad S.A.W. Ya Allah yai masa salati da alayensa da sahabansa bakidaya da mabiyansu har zuwa ranar lahira.
Bayan munyi sallar asuba mukanyi yan lazumai kan rana ta kusa fitowa sai mu koma mu dan kishingida kan lokacin fita aiki. ina kwance cikin daki na baccin ya dan daukeni sai naji bugawar daki, na tashi da sauri na bude na dauka Babana ne yazo yana bugamu yaga zan makara fita aiki..budewa ke da wuya sai naga kani na naga aron jama'a a kofar gida, nan take kanena yace kai sauri ka canza kaya mu tafi asibii baban mu ba lafiya...nan ake nai sauri nasa kaya na nafito. na shiga gaban mota kanne na na baya sun sa babanmu a tsakiya suna rikeshi jikinsa na langabewa.
muka kama hanyar katsina road zamu kaishi asibitin khadija memorial hospital, tun kafin muyi nisa naga hakoransa sun rufe da harshensa jiki, nacewa kane na ya bude bakin ya maida masa, nan take yamaida masa, isarmu asibitin keda wuya muka fio dashi da sauri muka kamashi da kannena muka shigar dashi cikin asibitin mukai sa'a docor Gambari yana na, Dan danan yace mu shigar dashi ofishinsa na E.P.C dakin ganin mara lafiya na gaggawa. yaransa suka kama muka shiga dakin tare,,nan ake ya dakko kayan gwaje gwajen mara lafiya yana aunashi, nan ake naga doctor Gambari ya kalleni ya girgiza kai yace ''am sory'' kuyi hakuri,,na tasi da fada inawa doctor tsawa: malam munkawo maka shi ka duba mana kai masa magani baka da kayan aiki ne daga ajeci a daki ka auna sai kace mana muyi hakuri me kake nufi!? Ko dan kaga munzo asibitin ka kaitsaye a rude? nai kamar na daki docotor ,yan'uwana kuma sai kuka sukeyi ina ce masu ku dena kuka karya yake mana bai mutu ba.,,na dora hannuna kan kirjinsa ina dannawa da karfi ina cewa ka farka baba, ina ta dannara da karfi muane suka leqo sunata kallona, har na gani jikina yai sanyi, yan'uwana sukazo suka janyeni, dacotor yasa aka daukeshiaka kwantar dashi dakin aje marasa laciya,,,duk da haka sai na tashi na shiga dakin ina bude fuskarsa ko zanga ya farfado, daga karshe dan nasa hannu na shafa fuskarsa na rufe masa idanunsa.
safiyar da ba zan aba mantawa da ita ba kenan a rayuwata har Allah ya dauki raina na je na tarar da mahaifina.
ya Allah ka jikansa ka gafarta masa kasa ya huta kasadamu dashi a jannatul firdausi. ka haskaka qabarinsa ka sadashi da masoyinsa Anabi muhammad S.A.W. Ameen.

