Monday, 22 February 2016

So Dan Allah

IDAN ZA KA SO MUTUM KA SO SHI DAN ALLAH.

Ya Allah bamu da Sani Sai abun da
Ka sanar da mu.

Ta Yaya mutun zai gane soyayar da ya ke wa dan'uwànsa da Allah ya ke mai?

Allah SWT ya halicci dan Adam ya sanya mai gani da Ido da Ji na Kunne da Ji na Jikin Fatar-Jiki da Shaqa ta Hanci da Dandano ta Hàrsahe.

Sannan ya halicci Zuciya da Kwawalwa ya sanya su ne ke aikin tantamce dukkan wani Motsi ko Yanayi da Ido zai gani ko Kunne ya ji/saurara, ko ya taba Jiki, ko hanci ya shaqa.

Allah s.w.t ya sanyawa Zuciya aikin da ya fi na dukkan sauran gabobin jiki.

Dare da rana tsawon rayuwar dan Adam a doron Duniya aikin zuciya baya tsayawa, walau Bacci ne ko a Farke.

Wala'alla a ce ita kwakwalwa aikinta kan tsaya idan mutum ya yi Bacci. Amma wasu lokutan sukanyi aiki da zuciya koda mutum ya na Bacci kamar yanda mu ke tabbatar da hakan a mafarki yayin da mu ke yin Bacci.

Kamar dai yanda Masana su ka tabbatar aikin zuciya da kwakwalwa baya tsayawa a farke ko a Bacci domin kuwa in muka duba yanda mutum in ya na yin Bacci ya kan yi Murgineneniya daga Dama zuwa Hagu zuwa Rubda-ciki, Wanda hakan na nuni ne da cewa duk sanda Mutum ya canja Sashen kwanciya, daya sashen ne ya gaji ya na bukatar samun sauki.

Anan kaga kenan zuciya da kwakwalwa ne su kai aiki tare bayan Isar saqon gajiya da zuciya ta aikawa kwakwalwa.

Wannan Doguwar Shimfida kamar Hanya ce da za ta kewayo da mu, Ta hada mu da zancen da mu ka fara yi a baya.

Zuciya kan ji wasu abubuwa da suka hada da So, Qi, Tsoro, Murna/Farin-ciki, Damuwa, Baqin-Ciki ds.

Soyayya Wani yanayi ne a boye cikin Zuciya  da mutum zai iya amfani da tunaninshi ya tantance nau'in da ke tattare da ita.

Kamar yanda ido zai iya banbance tsakanin dare da rana ko tsakanin Fari da Baqi, Ja da Kore.

Ko Kamar yanda Kunne zai Tantance Kukan Jaki Da Haniniyar Doki, Ko Carar Zakara da Da Qatar Shaho.

Ko Kamar Yanda Fatar Jiki za ta Banbance Iska mai Zafi da Iska mai Sanyi. Ruwan zafi ko Ruwan Sanyi.

Ko kamar yanda Hanci ke Tantance Wari da Qamshi.

Harshe kuma ke Tantance tsakanin Daci Da Zaqi.

Idan Har ba zamuyi Musun wayencen aiyyuka na dukkan gabbobin da Allah ya horewa dan'adam ba Wanda gabobi ke kaiwa kwakwalwa saqon aukuwar wani abu.

To ya zama wajibi mu yadda da cewa Dan'adam da kansa zai iya Tantance irin yanayin Soyayyar da ke cikin Zuciyarsa da ya ke wa dan'uwansa ta hanyar tsayawa da kyau ai tunani.

Yayin da Dan Adam ya ji ya na son wani dan adam, ma'uninan da zai auna ya gane ko son da ya ke wane iri ne su ne:

- Shin me ne ne dalilin da ya sa na ji son shi cikin zuciya ta?

- Ina da Wata masalaha ta karan-kaina da na ke Buqata daga wajenasa ko kuma ya yi wa wani makusanci na?

- Shin wayenne abubuwa ya aikata da har ya burgeni na ji ina son sa?

- Ayyukan da ya yi Masu anfanar da ni karan-kaina ne ko wani nawa ko gaba-daya.

Lamarimn a Bayyane ya ke idan ka Bari kwakwalwarka tai aiki da sikelinta da kyau.

1. Duk son da za kaiwa mutum mai kyautatawa wa su daban  ba kai ba. Ya na da ga cikin so dan Allah

2.  Duk son da zakaiwa wani bawan Allah ba dan ya ma komai Ba Sai dan ya na riqo da Addini, yana son Allah da manzonsa ya na yawa ita ibada. Ya na daga cikin soyayya dan Allah.

3. Duk son da za ka ji ka na son Son Mutumin da ya taba kyautata ma ka kuma ko da ya de na kyautata ma kan kaji ka na son shi. Wannan ma yana daga cikin so dan Allah.

4. Ya kan kasance Ba ka taba ganin Mutum ba Sai dai labarin kyawawan halayensa da dabi'unsa kawai ka ji amma ka ji ka na son shi.

Wannan ma ya na daga cikin soyayya dan Allah.

Idan mu ka duba cikin hadisin Annabi S.A.W . ya zo da cewa:

"An halicci zuciya da son Wanda ya kyautata ma ta, sanna kuma yana kin Wanda ya munana mata."

Abun nuni a nan shi ne duk Wanda ka yiwa kyakkyawar mu'amala zai so ka duk Wanda kai wa mummunar mu'amala zai tsane ka.

 Haka nan ka kan so mutumin da ka ji labarin kyawawan halayensa ko kuma ka ji haushi duk Wanda ka ji munanan dabi'unsa.

Tambihi:-

- Soyayya da ake yi dan ka na neman wani abu wajen wani, ta zama Ba dan Allah ba domin idan Ba ka samu biyan bukata Ba karshe ta koma qiyayya.

- Dan Haka so na dan Allah baya bukatar sanya wani Burace-burace a cikinta.

- Mu dauki Hadisin Umar Bini Khaddabi R.A da ya ji daga Annabi S.A.W.

"Dukkan ayyuka su na Farawa ne daga Niyyar  aikatasu, Wanda yai Qaura zuwa ga Allah da manzonsa, to ya yi Qaurar ta sa ne dan Allah da manzonsa. Wanda kuma yai Qaura dan Wani abun Duniya kuma ya samu, ko dan Macen da ya ke so ya aura, To ya yi Qaurarsa ne Dan Duniya kawai."
[Bukhari da Muslim]

Wannan hadisi ya na nuni da abubuwa da dama da Masu tawili suka bayyana.

amma kan maganar da na ke yi yanzu shi ne so dan Allah.

Niyya ita ce Tushen shi, domin dukkan Niyyar aikata wani abu daga cikinta ta ce fadawa.

Dan haka duk yayin da ka ke son wani to ka auna mafarin son a sikelin zuciya da kwakwalwa dan ka gane irin son da ka kamu da shi, kamar yanda na bayyana a baya.

Allah shi yafi kowa sani. Allah ya kara mana fahimta, ka nuna mana gaskiya tare da ikon binta.

Dalibi: BASHIR ABBAS DALHATU.

Tuesday, 26 August 2014

GA ALLAH MUKE GARESHI ZAMU KOMA!!!

RANA MAFI KUNCI A RAYUWATA.

Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga mahaliccin duniyoyi wanda ya aiko manzonsa muhammad S.A.W zuwa doniya bakidaya. tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta Annabi muhammad S.A.W. Ya Allah yai masa salati da alayensa da sahabansa bakidaya da mabiyansu har zuwa ranar lahira.

Bayan munyi sallar asuba mukanyi yan lazumai kan rana ta kusa fitowa sai mu koma mu dan kishingida kan lokacin fita aiki. ina kwance cikin daki na baccin ya dan daukeni sai naji bugawar daki, na tashi da sauri na bude na dauka Babana ne yazo yana bugamu yaga zan makara fita aiki..budewa ke da wuya sai naga kani na naga aron jama'a a kofar gida, nan take kanena yace kai sauri ka canza kaya mu tafi asibii baban mu ba lafiya...nan ake nai sauri nasa kaya na nafito. na shiga gaban mota kanne na na baya sun sa babanmu a tsakiya suna rikeshi jikinsa na langabewa.
muka kama hanyar katsina road zamu kaishi asibitin khadija memorial hospital, tun kafin muyi nisa naga hakoransa sun rufe da harshensa jiki, nacewa kane na ya bude bakin ya maida masa, nan take yamaida masa, isarmu asibitin keda wuya muka fio dashi da sauri muka kamashi da kannena muka shigar dashi cikin asibitin mukai sa'a docor Gambari yana na, Dan danan yace mu shigar dashi ofishinsa na E.P.C dakin ganin mara lafiya na gaggawa. yaransa suka kama muka shiga dakin tare,,nan ake ya dakko kayan gwaje gwajen mara lafiya yana aunashi, nan ake naga doctor Gambari ya kalleni ya girgiza kai yace ''am sory'' kuyi hakuri,,na tasi da fada inawa doctor tsawa: malam munkawo maka shi ka duba mana kai masa magani baka da kayan aiki ne daga ajeci a daki ka auna sai kace mana muyi hakuri me kake nufi!? Ko dan kaga munzo asibitin ka kaitsaye a rude? nai kamar na daki docotor ,yan'uwana kuma sai kuka sukeyi ina ce masu ku dena kuka karya yake mana bai mutu ba.,,na dora hannuna kan kirjinsa ina dannawa da karfi ina cewa ka farka baba, ina ta dannara da karfi muane suka leqo sunata kallona, har na gani jikina yai sanyi, yan'uwana sukazo suka janyeni, dacotor yasa aka daukeshiaka kwantar dashi dakin aje marasa laciya,,,duk da haka sai na tashi na shiga dakin ina bude fuskarsa ko zanga ya farfado, daga karshe dan nasa hannu na shafa fuskarsa na rufe masa idanunsa.

safiyar da ba zan aba mantawa da ita ba kenan a rayuwata har Allah ya dauki raina na je na tarar da mahaifina.
ya Allah ka jikansa ka gafarta masa kasa ya huta kasadamu dashi a jannatul firdausi. ka haskaka qabarinsa ka sadashi da masoyinsa Anabi muhammad S.A.W. Ameen.

Saturday, 22 February 2014

تهاني على هادي والنفيسة Congratulations to Hadi and Nafisa for their wedding.may God bless